LibraryBelgeler
Matsayin Musulmi a wajen ‘Yan Shi’a
littafin yana magana ne akan Matsayin Musulmi a wajen ‘Yan Shi’ada sauran abubuwa masu mahimmaci saninsu By: Umar Muhammad Labdo Source: IslamHouse.com · Umar Muhammad Labdo
Kitaptan
Metnin ilk sayfaları. Tamamını okumak için yukarıdaki kitabı açın.
1
Jerin Littafan Shi’a Na 5
Matsayin
Musulmi
a wajen
‘Yan Shi’a
Umar Labxo
2
بسم هللا الرحمن الرحيم
Gabatarwa
Lallai godiya ta tabbata ga Allah, muna gode masa, muna neman
taimakonsa, muna neman gafara tasa. Muna neman tsari da Allah daga
sharrin kawunanmu da miyagun ayyukanmu. Wanda Allah ya shirye shi,
babu mai vatar da shi kuma wanda ya vatar babu mai shiriya tasa. Ina
shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kaxai, ba shi da
abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa Muhammad bawansa ne, kuma
Ma’aikinsa ne. Tsira da aminci su tabbata a gare shi, da Alayensa, da
Sahabbansa, da waxanda suka bi Sunnarsa har zuwa ranar sakamako.
Bayan haka, ‘yan Shi’a suna yawan yin magana dangane da haxin kan
Musulmi. Ba sa barin wata munasaba ta wuce ba tare da sun maimaita kira
izuwa haxin kai ba, da sukan rarraba da karkasuwa zuwa qungiyoyi da
mazhabobi. Sau da yawa sukan yi kira da haxin kai tsakaninsu da Ahalus
Sunna, suna masu qarfafa cewa bai kamata a samu savani ba domin hakan
yana raunana Musulmi a gaban abokan gabansu. A wasu lokuta sukan nuna
cewa abubuwan da suka raba su da Ahalus Sunna ba wasu muhimmai ba ne,
kuma su da Ahalus Sunna duka abu guda ne tunda Shi’a ita ma mazhaba ce
kamar sauran mazhabobi.
A wasu qasashe, ‘yan Shi’a suna kira da abinda suke wa laqabi da
Attaqrib bainal Mazahib, ko kuma Atta’aruf, watau kusantar da mazhabobi
ga junansu ko kuma fahimtar juna, suna nufin kusanci da fahimtar juna
tsakanin tafarkin Shi’a da na Sunna. A nan Nijeriya kuwa, mun san su da
kirarin Islam One, wanda suke bin gine-ginen hukuma kamar makarantu da
ofisoshi suna rubutawa, wai suna nufin Musulunci xaya ne, babu bambanci
tsakanin wani tafarki da wani, ko kuma wata mazhaba da wata.
Amma mene ne haqiqanin abinda ‘yan Shi’a suka xauki mai bin
tafarkin da ba nasu ba, musamman Ahalus Sunna? Shin gaskiya ne suna
xaukar dukkan Musulmi xaya ne, ko kuwa kawai yaudara ce suke yi don su
samu karvuwa a wajen mutane? Mene ne abinda manyan malaman Shi’a
suke faxi dangane da Ahalus Sunna, da sauran Musulmi duka, a da da kuma
yanzu? Shin sun yarda su Musulmi ne kamar yadda su ma suke da’awar
Musulunci, ko kuwa suna xaukar su dabam? Ya suka xauki imaninsu da
3
sallarsu da azuminsu da hajjinsu da yankansu da auratayyarsu da sauran
ma’amalolinsu da ayyukansu na addini?
Wannan xan qaramin littafi zai yi qoqarin amsa waxannan
tambayoyi, da ma wasunsu, in Allah ya yarda, kuma amsoshin duka za su
fito kai tsaye daga bakin manyan malaman ‘yan Shi’a, ta hanyar littafansu
waxanda suka yarda da su. A qarshe mai karatu zai fita da sahihiyar fahimta
ta matsayin Ahalus Sunna, da sauran Musulmi, a wajen ‘yan Shi’a ta yadda
zai yi hukunci da kansa a kan wannan da’awa ta Rafilawa ta kira zuwa ga
haxin kai da kusanto da mazhabobi da fahimtar juna idan gaskiya ce ko
kuwa qarya ce da yaudara.
Manufarmu a nan, in Allah ya yarda, ita ce bayanin gaskiya da sauke
nauyin da yake kanmu na al’ummarmu, don wanda ya halaka ya halaka a
bisa sani kuma wanda ya shiriya ya shiriya a bisa sani. Kuma gamon
katarinmu bai zamo ba sai ga Allah, a gare shi muke dogara, kuma gare shi
muke komawa.
Yorumlar
Henüz yorum yok. Faydalı bir düşünceyi ilk paylaşan siz olun.
İlgili
Matsayin Mace Musulma Wajen Gina Iyali Nagari
islamicmedia.tv
5 views · 1 month ago
Matsayin Mata A Musulunci, Yahudanci da Nasaranci
islamicmedia.tv
7 views · 5 months ago
Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alkur’ani Da Sunna
islamicmedia.tv
7 views · 5 months ago
garkuwan musulmi
islamicmedia.tv
6 views · 5 months ago
ƘAYATA GURAREN ZAMA Taƙaitattun Darussa cikin abubuwan da bai kamata Musulmi ya jahilce su ba.
islamicmedia.tv
5 views · 5 months ago
abinda bai kamata musulmi ya jahilta acikin addinin sa ba
islamicmedia.tv
6 views · 5 months ago
MATSAYIN SALLAH A CIKIN MUSULUNCI Ma'anarta, Hukuncinta, Abubuwan da ta kebanta da su, Hukuncin wand
islamicmedia.tv
7 views · 5 months ago
Wajabcin Yaqar Bidi’a
islamicmedia.tv
6 views · 5 months ago
Mugun Nufin ‘Yan Shi’a ga Al’umma
islamicmedia.tv
5 views · 5 months ago
Aqidar Ahalus Sunna
islamicmedia.tv
4 views · 5 months ago