LibraryDocuments
WASU HADISAI ARBA'IN GAME DA AL-QUR'ANI
WASU HADISAI ARBA'IN GAME DA AL-QUR'ANI Source: IslamHouse.com
Extrait du livre
Les premières pages du texte. Ouvrez le livre ci-dessus pour le lire en entier.
WASU HADISAI ARBA'IN GAME DA AL-
QUR'ANI
Wallafar
Ahmad Bn Abdurrazaq Bn Muhammad Aal Ibrahim Al-anazy
Gabatarwar
Babban Malamin Hadisi
Salih Bn Sa'ad Al'luhaidan
Da kuma Babban Malamin Hadisi
Abdullahi Bn Abdurrahman Al-Sa'ad
Kuma Babban Malamin Hadisi Dr.
Mahir Bn Yasin Al-fahl
Kuma Babban Malami Dr.
Hamad Al-tamimi
Bugu na sha biyar
Gabatarwar Muftin Alkali na Musamman Shehin
Malamin Hadisin nan: Salih Bn Sa'ad Al-
luhaidan - Allah Madaukaki ya kare shi -
Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin kai
Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya saukar da littafin sa Mai Hikima da kuma Shiriya Hukunci Gaskiya
da kuma Tafarki Madaidaici.An Saukar da shi ga Mafificin Halittarsa da Manzanninsa - Amincin Allah a
gare su - Annabi Muhammad tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi don ya tsaya wajen isar da
shi ga baki dayan su har zuwa ranar da za'a tashe su.Bayan Wannan Hakika Dana Shiekh Ahmad Bn
Abdurrazak Bn Muhammad Bn Zayid Al-angari ya gabatar mun kwafi na littafinsa HADISAI ARBA'IN
GAME DA AL-QUR'ANI wanda ya kunshi Falalolin Alqur'ani Maigirma da kuma abin da ya a san shi da
kuma aiki da shi ta hanyar Iklasi da gasgata aiki da kuma kubutacciyar Niyya ga barin abin da zai bata
ta.Kuma babu wani laifi to duk wanda yayi duba na nutsuwa ga abinda Shiekh Ahmad ya kawo a
littafinsa zai same shi cewa ana matukar bukatar kwatankwacin irin wannan a wannan lokaci wanda ya
yake bukatarsa, Ya wajaba ga Musulmi ya sani kuma ya kiyaye hakikanin Hukunce hukuncen Addininsa
da Duniyarsa ta hanyar Alqur'ani da Ingantacciyar Sunnakuma hakika ya zo daga Dan Umar cewa shi
ya ce: bama wuce Ayoyi goma har sai mun koyi Ilimi da kuma aiki da shi daga cikin suKuma Alqurani
Maigirma da Sunnanar Annabi dole ne a koye su daga Bakin Malamai wadan da suka hada tsakanin
Ilimi da Hadda da kuma Fahimta da kyakkyawar fahimta ta hakikanin abin da nassi yake nufi cikin
manufofin Rayuwar Duniya da lahira na abinda ya hada tsakanin Maganganu da kuma Ayyuka
kuma Rubuta wadan nan hadisan Alqurani bana zaton Shiekh Ahmad yana nufin ya gama tare baki
dayansu domin wasu daban da yawa sun zo suna nan a tattare a cikin Manyan litattafan Hadisi guda
Shida da wajensu Kamar Musnad na Imam Ahmad da Al-musannaf Na Abdurrazak da Musannaf na
Ibn Abi Shaibah, da Sahihin ibn Hibban da Musnad na Sa'id Bn Masour da wasun su na tushen
Musulunci, sai dai yana nufin fadakarwa zuwa Muhimmanci da kuma falalarsa da haddace shi da kuma
kyakkyawan Nazarinsa ta hanyar wa'azantuwa da Ayoyinsa ba wai don tarawa ba da kuma haddace
shi da aikata shi da Hukunci da abinda yake faruwa na Hukunce Hukuncen Sababbin abubuwa sababbi
da suke faruwa.
kuma ya isa Daukaka ga Mahaddacin Qur'ani cewa shi ana bashi lada kan Haddarsa , kuma qurani zai
cece shi, kuma ana samun waraka da shi kuma ana samun Albarkar samunsa da shi daidai da yadda
ya kyautata niyyarsa da kuma jin Tsoransa da tsantseninsa.
To Allah Madaukaki yayi Albarka a kokarin Shiekh Ahmad Al-Ibrahim Al-Angary kuma ya amfanar da
Ilimin sa kuma ya kuma Karfafe shi domin cewa shi Mai yawan kyauta ne kuma Mai baiwa
Wanda ya rubuta shi
Salih Bn Sa'ad Al'luhaidan
1428/1/17 Bayan Hijira
Gabatarwar Shehin Malami Masanin Hadisi
Abdullahi Bn Abdurrahaman Al-sa'ad - Allah ya
tsare shi -
Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin kai
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai kuma tsira da Aminci su tabbata ga Manzon Allah tsira da
Aminci su tabbata a gare shi. Bayan haka kuma
To hakika na karanta littafin Dan mu Shiekh Ahmad Bn Abdurrazak Bn Muhammad Al-Ibrahim Al-
angary Allah ya datar da shi.
wacce ta tare Hadisai Arba'in na Falaloli da Hukunce Hukunce da kuma Ladaban Alqur'ani Maigirma,
kuma hakika ya kyautata wajen taro su kuma ya amfanar, to Allah ya saka masa da Alkairi.
kuma wannan Maudu'i yana daga cikin Maudu'ai Muhimmai sabo da dangantakar sa da littafin Allah
Maigirma da Daukaka
Kuma daga cikin Mafi girman Ayyukan neman lada wadan da Bawa zai kusanci Ubangijinsa da su
Nazarin Ayayoyinsa kamar yadda Allah yace cikin littafinsa: "Littafi ne da muka saukar da shi a gareka
mai Albarka don kuyi nazarin Ayoyinsa"
Ibn Al-qayyim ya ce: a cikin Fa'idodi: littafi na 1 a shafi na 3Wata Babbar Ka'idaIdan kanason Amfani
da Qur'ani to ka taro zuciyarka wajen Karatunsa da jinsa, kuma kabada jinka, ka halarto da zuciyarka
da wanda kake magana da shi mai tsarki, to cewa zancensa, wanda yazo ta hanyar Manzonsa.Allah
Madaukaki ya ce"Lalle ne, a cikin wancan, akwai tunãtarwa ga wanda zũciyarsa ta kasance gare shi,
kõ kuwa ya jẽfa saurãro, alhãli kuwa yanã halarce (da hankalinsa).Suratu Kaaf: 37
kuma wannan cewa cikar Tasirin ya kasance yana nan ne kan Tasirin abun da ake karantawa, kuma
nan Mahallin karba, kuma Sharadin samun Tasirin, kuma da kore duk wani abun da zai hana hakan,
kuma Ayar ta kunshi bayanin hakan baki dayan sa da dunkulallun lafazansa da gininsa, da kuma
nuninsa kan Manufarsa.
Da fadinsa: Lalle ne, a cikin wancan, akwai tunãtarwaSurat Kaaf: 37Nuni zuwa ga abinda ya gabata
daga farkon Sura zuwa nan kuma wannan shi ne abu mai TasiriFadinsa:Ga duk wanda yake da Zuciya
(ta hankalta).To wannan shi ne Mahallin da zai karba, kuma abin nufi da shi shi ne Zuciya Rayayyiya
wacce take fahimtar sakon AllahKamar yadda Allah Madaukakin Sarki ya ce:Lallai cikin wann nan ba
komai ba ne face wa'azi sa kuma Qur'ani mai bayani domin a wa'azantar da RayayyeAi mai rayayyiyar
zuciyaSannan fadinsako wanda aka jefa masa jiAi wanda ya bada jinsa kuma yai saurara da jinsa zuwa
abinda ake fada a gare shi, kuma wannan sharadin yana tasiri wajen maganaSannan fadinsakuma
yana mai halarto da ZuciyarsaAi yana mai harto da a Zuciyarsa baya kautar da itaIbn Kutaibah ya ce:Ka
saurari Littafin Allah kuma yana mai halarto da Zuciyarsa da fahimta baya rafkana ko mantuwakuma
wan nan yana nuni zuwa abin da yake hana tasirantuwa, kuma shi ne rafkanar zuciya da buyanta ga
barin fahimtar abinda ake fada mata da kuma Nazari a cikinsa da yin kyakkayawan Duba to idan aka
samu maisa tasirin shi ne Al'qur'ani kuma aka samu wurin karba shi ne zuciya rayayyiya, kuma aka
samu sharadin shi ne saurararawa, kuma aka kore Mai hanawa shi ne shagaltuwar zuciya da kuma
sakwarkwacewar ta daga Ma'anar Kira, da kuma kaucewarsa daga kan turba zuwa wani abu daban,
sai tasirin ya faru shi ne anfanuwa da kuma wa'azantuwa.
Ina rokon Allah da ya amfanar da wannan littafin kuma ya sanya shi mai albarka kuma ya datar da
Marubucinsa ga dukkan Alkairi
Tsira da Aminci ga Annabinmu Muhammad
Wanda ya rubuta shi: Abdullahi Bn Abdurrahaman Al'sa'ad
17/3/1428 Bayan Hijira
Gabatarwa Babban Malami Masanin Hadisi Dr.
Mahir Bn Yaseen Al'fahl Allah ya tsare shi
Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin kai
Dukkan Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin Talikai kuma tsira da Aminci su tabbat ga Shugabanmu
Annabi Muhammad da Alayansa da Sahabbansa baki Daya
Bayan haka
To lallai wajibin kira zuwa ga Allah yana daga cikin Mafi Cancantar Wajibai, kuma mafi wajabcin Biyayya
ga AllahKuma Allah Madaukakin Sarki ya ce: "Babu wata Magana mafi kyau kamar wanda yayi kira
zuwa ga Allah kuma yayi aiki nagari kuma ya ce yana cikin Musulmi.Surat Fussilat 33To ya wajaba
akan kowane Musulmi cewa ya tsaya da wannan Wajibin na Addini ga Al'ummarsaAllah Madaukakin
Commentaires
Aucun commentaire pour l'instant. Soyez le premier à partager une réflexion utile.
À voir aussi
HADISAI 100 DOMIN HADDA
islamicmedia.tv
6 views · 5 months ago
عظماء في التاريخ
islamicmedia.tv
1 view · 8 hours ago
من أحكام صلاة المرأة في الحرمين
islamicmedia.tv
1 view · 8 hours ago
البرنامج اليومي للمسلمة في شهر رمضان
islamicmedia.tv
1 view · 8 hours ago
أحكام المرأة في الصلاة دراسة فقهية مقارنة
islamicmedia.tv
1 view · 8 hours ago
توحيد الألوهية أساس الإسلام
islamicmedia.tv
1 view · 8 hours ago
شرح رسالة القواعد الأربع
islamicmedia.tv
1 view · 8 hours ago
توحيد الرب
islamicmedia.tv
1 view · 8 hours ago
شرح خطبة الحاجة
islamicmedia.tv
1 view · 8 hours ago
إِلاَّ لِيَعْبُدُونِ - كيف يوحد القرآن وجهة الإنسان؟
islamicmedia.tv
1 view · 8 hours ago