Libraryوثائق
WAJABCIN AIKI DA SUNNAR ANNBIN ALLAH TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARESHI DA KAFIRCIN WANDA Y
WAJABCIN AIKI DA SUNNAR ANNBIN ALLAH TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARESHI DA KAFIRCIN WANDA YA MUSANTA HAKAN By: abdul aziz bin abdaal bin baz Source: IslamHouse.com · abdul aziz bin abdaal bin baz
من الكتاب
الصفحات الأولى من النص. افتح الكتاب أعلاه لقراءته كاملًا.
WAJABCIN AIKI DA SUNNAR ANNBIN
ALLAH TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU
TABBATA A GARESHI DA KAFIRCIN WANDA
YA MUSANTA HAKAN
Wallafar
Shehin Malami
AbdulAzeez Bin Abdullahi Bn Baaz
Allah ya yi masa Rahama
3
Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin kai
Gabatarwa
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin TalikaiKuma kyakkyawan karshe ya tabbata
ga masu jin tsoron AllahKuma tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Bawansa
kuma manzonsa Annabi Muhammad wanda aka turo shi ya zamo rahama ga
dukkannin halittu ,ya kuma zamo hujja ga Daukacin bayin Allah baki daya.Kuma da
Iyalansa da kuma Sahabbansa wadanda suka riki littafin Ubanngijin su da sunnar
Annabinsu tsira da aminci su kara tabbata a gare shi har zuwa ga wadan da suka
zo a bayansu da amana da cikakkiyar kiyayewa ga ma’anoni da laffuza yardar Allah
ta qara tabbata a garesu Allah ya sanya mu daga cikin wadanda zasu biyo bayansu
da kyautatawa
Bayan haka
To hakika Malamai Ra'ayinsu ya zo daya na da da na yanzu kan cewa Ginshikin
abubuwan da ake lura da su wajen tabbatar da Hukunci, da kuma bayanin Halal da
Haram cikin littafin Allah Mabuwayi wanda Barna bata iya shiga cikin sa ta gaba ko
ta bayansa.san nan sunnar Manzon Allah tsira da aminci su qara tabbata a gare shi
Wanda baya Magana akan son zuciya sai kadai abinda aka yi masa wahayin
shi.San nan abin da manyan Maiamai suka hadu akan shi akwai kuma wasu tushen
da Malamai suka yi sabani akan su mafi muhimmanci shi ne kiyasi amma mafi
yawan su sun tafi akan cewa hujjane idan ya cika dukkanin sharudan da suka
kamataKuma dalilai akan haka suna da yawa yawan da ba za su Kididdugu ba mafi
shahara daga cikin su su ne
Tushen da suke bayani kan tabbatar da hukunce
hukunce
Tushe na farko: shine littafin Allah mabuwayi
Amma tushen farko: shine littafin Allah mabuwayi
kuma hakika zancen Ubangiji ya nuna a wurare da yawa na littafin Allah kan
wajabcin bin wannan littafin da kuma riko da shi da tsayuwa akan dokokinsa.
Allah Madaukaki ya ce
Ku bi abin da aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku, kuma kada ku dinga bin
wasu majiɓinta baicinSa. Kaɗan ƙwarai kuke tunãwa.
kuma Allah Madaukaki ya ce
4
Kuma wannan Littãfi ne, Mun saukar da shi, mai albarka ne, sai ku bĩ shi kuma ku
yi taƙawa, tsammãninku, anã jin ƙanku.
kuma Allah Madaukaki ya ce
Haqiqa Manzon Mu yã je muku, yanã bayyana muku abu mai yawa daga abin da
kuka kasance kunã ɓõyewa daga Littãfi, kuma yanã rangwame daga abu mai yawa.
Haƙĩƙa, wani haske da wani Littafi mai bayyanãwa yã je muku daga Allah.
Dashĩ, Allah Yanã shiryar da wanda ya bi yardarsa zuwa ga hanyõyin aminci, kuma
Yanã fitar da su daga duffai zuwa ga haske da izninsa, kuma Yanã shiryar da su
zuwa ga hanya madaidaiciya.
kuma Allah Madaukaki ya ce
Waɗannan da suka kãfirta game da Alkur'ãni a lõkacin da ya je musu, kuma lalle
shi haƙĩƙa littãfi ne mabuwãyi.
arna bã zã ta je masa ba daga gaba gare shi. kuma bã zã ta zo ba daga bãya gare
shi. Saukarwa ce daga Mai hikima, Gõdadde.
kuma Allah Madaukaki ya ce
’An yi min wahayin Wannan Alqur’anin dan na gargade ku dashi wa ye ya isar
kuma Allah Madaukaki ya ce
Wannan Sako ne ga Mutane kuma don ayi musu gargadi da shi
Ayoyin da suka zo da wadannan ma’anonin suna da yawa Hadisai ingantattu sun
zo daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi da suke
umarni da riko da Alqur’ani da tsare shi suna nuni da cewa wanda duk yayi riko da
shi to hakika yana kan shiriya wanda duk ya bar shi kuma haqiqa yana kan bata
Daga wannan da wani abinda ya tabbata daga Annabi tsira da aminci su qara
tabbata a gare shi, yana cewa a cikin Hudubarsa ta Bankwana :
’Hakika na bar muku abinda in kun rike shi ba zaku Bata ba ku yi riko da Littafin
Allah
Muslim ya rawaito shi a cikin Sahih din sa
Acikin Sahih Muslim ya rawaito kuma cewa Zaidu dan Arqam Allah ya qara yarda
da shi cewa Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi yana cewa:
Lallai na bar muku abubuwa biyu Littafin Allah cikinsa akwai shiriya da kuma Haske
to ku riki littafin Allah kuma kuyi riko da shi.
Ya kwadaitar a kan Littafin Allah san nan yace:
التعليقات
لا توجد تعليقات بعد. كن أول من يشارك بتأمّل نافع.
ذات صلة
Manzon Musulunci Annabi Muhammad ( tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi)
islamicmedia.tv
8 views · 5 months ago
"TATACCIYAR BAKANDAMIYAR HADISAN ANNABI" (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi)
islamicmedia.tv
6 views · 5 months ago
Manzon Musulunci Annabi Muhammad - tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi
islamicmedia.tv
6 views · 5 months ago
QISSAR ANNABI ISA -AMINCIN ALLAH A GARE SHI- DAGA CIKIN AL-QUR'ANI MAI GIRMA
islamicmedia.tv
5 views · 5 months ago
Wajabcin Yaqar Bidi’a
islamicmedia.tv
6 views · 5 months ago
TABBATARWA DA BAYYANA YAWANCIN MAS'ALOLIN HAJJI DA UMRA DA KUMA ZIYARA AKAN DORON LITTAFI DA SUNNAH
islamicmedia.tv
7 views · 5 months ago
Hukuncin Sihiri Da Bokanci
islamicmedia.tv
5 views · 5 months ago
TAƘAITATTUN SAƘONNI BIYU A KAN ZAKKA DA AZUMI
islamicmedia.tv
5 views · 5 months ago
SIFFAR SALLAR ANNABI
islamicmedia.tv
4 views · 5 months ago
SIFFAR AIKIN UMARA
islamicmedia.tv
5 views · 5 months ago