Kitaptan
Metnin ilk sayfaları. Tamamını okumak için yukarıdaki kitabı açın.
1
Maganar Gaskiya Dangane Da
Zancen Haxin Kai
Daga
Dr. Nasir Ibn Abdallah Alqifárí
2
Maganar Gaskiya Dangane Da Zancen Haxin Kai
Daga
Dr. Nasir Ibn Abdallah Alqifárí
Qoqarin rage tazarar da take tsakanin qungiyoyin addini, da haxa
kansu, ba wani abu yake nufi ba, illa tattara su wuri xaya a kan tafarkin
gaskiya bisa zimmar karvawa da cika umarnin Allah Maxaukakin Sarki,
a cikin faxarsa: “Kuma ku yi riqo da igiyar Allah gaba xaya; kuma kada
ku rarraba.” {Áli- Imran:103}. Wannan aiki kuma yana xaya daga cikin
manya farillolin Musulunci da manufofinsa.
Sai dai matakin raba gardama a duk lokacin da ake jayayya a
kan wani abu, shi ne komawa ga Littafin Allah Maxaukakin Sarki,
Alqur’ani, da kuma Sunnar Annabinsa, sallallahu alaihi wa sallam,
kamar yadda Buwayayyen Sarkin ya bayyana cewa: “Idan kun yi
jayayya a cikin wani abu, to, ku mayar das hi zuwa ga Allah da
Manzonsa...” {Nisá’i: 59} Inda kuwa har babu maganin kowace irin
jayayya tsakanin Musulmi a cikin waxannan tuwasu guda biyu, to,
Allah Maxaukakin Sarki ba zai yi umarni da komawa zuwa gare su ba.
Sai dai babu wanda zai gane, balle ya ci moriyar wannan tsari
na Allah Maxaukakin Sarki, na santawa da haxa kan Musulmi, sai
wanda ya yarda ya kama tafarkin Littafin Allah da Sunnar Manzo, ya
kuma miqa wauya ga hukuncinsu, domin cewa Maxaukakin Sarkin ya
yi: “Kuma bay a halatta ga mumini, haka ga mumina, a lokacin da Allah
da Manzonsa suka hukunta wani umurni, wani zavi daga al’amarinsu ya
kasance a gare su. Wanda kuma ya sava wa Allah da Manzonsa, to, ya
vace, vacewa bayananna.” {Ahzáb:36}
Saboda haka, ba ya halasta ko alama! Saboda taqama, da sunan
haxin kai, a daidaita qarya da gaskiya, kamar yadda ba ya halasta a
daidaita matsayin bayin Allah masu nagarta da mavarnata, domin:
“Mummuna da mai kyau, ba su daidaita.” {Má’ida:100} “Kuma makaho
da mai gani ba su daidaita, waxanda kuma suka yi imani, suka aikata
ayyukan qwarai da mai munanawa, ba su daidaita. Kaxan qwarai kuke
yin tunani.” {Gáfir:58} Qoqari kuma da yunqurin daidai gaskiya da vata,
bayan zamansa abin dab a zai tava yiwuwa ba; abu ne kuma da zai
3
nakkasa gaskiya da masu ita. dalili kuwa shi ne, hakan za ta bayar da
hoton cewa, ai matsayin vata daidai yake da na gaskiya.
Haka kuma qoqarin rufe ido da kawar da kai daga tabbatattun
hujjoji, da daddalallin banbance-banbance a cikin kowane al’amari, abu
ne da ba ya biyan bukata. Haka abin yake kamar maras lafiya ne, ya
xauka cewa ai lafiyarsa qalau; ya warke. Saboda haka ba zai sake shan
magani ba, alhali kuwa ga ciwo yana cinsa a voye.
A taqaice duk wanda yake maganar haxin kai tsakanin
qungiyoyin addini, ba tare da ya koma ga tanade-tanaden Alqur’ani da
Sunna ba a kan wannan mas’alah, a matsayinsu na tuwasun asali,
waxanda wannan jama’a suke cirato dokokin aqidu da ayyukansu, to,
yana bannan kuskure. Dalili kuwa shi ne, a qa’idah ta usúlu, duk
hukuncin da za a yanke wa reshe, dole ya zamana ya samo asali daga
tushensa. Matsayin wannan mutum daidai yake da na wanda yake
cewa ai, babu wani banbanci tsakanin mazhabobin fiqihun Musulunci,
waxanda samo asali xaya a aqida da sauran hukunce-hukunce, kamar
mazhabobin nan na Musulunci guda huxu;1 da sauran qungiyoyi
waxanda suka sava wa tafarkin ahlu- Sunnah wal jamá’ah, ko ma har
da sauran rassan wannan al’umma kamar Ráfilawa da Jahmiyyawa.
Haka nan kuma, duk wanda yake cewa babu wani banbanci
tsakanin qaramar bidi’a, kamar karkata ga aqidun shi’ah ko ma
tsunduma a cikinsu gaba xaya, har da fin mai kola shafawa, kamar
yadda magabatan wannan al’uma suka fahimta; ya ce ba wani banbanci
tsakanin su da babbar bidi’a, kamar Rafilanci da sukar lamirin Sayyadi
Abubakar, da Umar, raliyallahu anhuma. Duk wanda yake da irin
wannan aqida, to, bai gane bakin zaren mas’alar ba. Wannan shi ne
abin da Imamuz- Zahbí,2 da Hafiz Ibnl Hajar3 da wasu malamai suka
bayyana.
To, sai ga shi a wannan zamani namu, irin wannan yamutsi na
haxa hancin gaskiya da na qarya, tare da kasa banbancewa a
tsakaninsu suna ta toroqo, wato ambaton “’Yan Shi’ah” da sunan
‘Rafilawa,” alhali kuwa a tantagar gaskiya, ambaton su da sunan ‘’Yan
koren Shi’ah’ ko ‘Yan koren Rafilanci’ shi ne gaskiya kuma daidai,
1 A duba littafin: Usulud-din Inda A’immatil- Arba’a Wahidatun, na Marubucin wannan takarda.
2 A duba: Mizanil- I’itidal, (1/5-6)
3 A duba: Lisanul- Mizan, (1/9-10).
Yorumlar
Henüz yorum yok. Faydalı bir düşünceyi ilk paylaşan siz olun.
İlgili
عظماء في التاريخ
islamicmedia.tv
1 view · 9 hours ago
من أحكام صلاة المرأة في الحرمين
islamicmedia.tv
1 view · 9 hours ago
البرنامج اليومي للمسلمة في شهر رمضان
islamicmedia.tv
1 view · 9 hours ago
أحكام المرأة في الصلاة دراسة فقهية مقارنة
islamicmedia.tv
1 view · 9 hours ago
توحيد الألوهية أساس الإسلام
islamicmedia.tv
1 view · 9 hours ago
شرح رسالة القواعد الأربع
islamicmedia.tv
1 view · 9 hours ago
توحيد الرب
islamicmedia.tv
1 view · 9 hours ago
شرح خطبة الحاجة
islamicmedia.tv
1 view · 9 hours ago
إِلاَّ لِيَعْبُدُونِ - كيف يوحد القرآن وجهة الإنسان؟
islamicmedia.tv
1 view · 9 hours ago
Resumo do livro Seleção de Hadiths Proféticos
islamicmedia.tv
1 view · 1 day ago