Libraryوثائق
ABIN ZABOWA DAGA ABIN KASUWANCI MAI RIBA A CIKIN LADAN AIKI NA GARI LADAN ILIMI DA NA MALAMAI
ABIN ZABOWA DAGA ABIN KASUWANCI MAI RIBA A CIKIN LADAN AIKI NA GARI LADAN ILIMI DA NA MALAMAI Source: IslamHouse.com
من الكتاب
الصفحات الأولى من النص. افتح الكتاب أعلاه لقراءته كاملًا.
Abin Zabowa Daga Abin
Kasuwanci Mai Riba A
Cikin Ladan Aiki Na Gari
3
Ladan Ilimi Da Na Malamai
Daga Mu'awiya - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Duk wanda Allah Ya ke nufin sa da alheri zai fahimtar da shi
Addini".
Bukharine ya ruwaito shi (71) da Muslim (1037).
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Wanda ya shiga wata hanya wacce ya ke neman ilimi a cikin ta
Allah Zai sauwaƙa masa hanyar zuwa Aljanna da ita, mutane ba za su
haɗu a wani ɗaki daga ɗakunan Allah ba, suna karanta littafin Allah,
suna dandaƙa karanta shi a tsakaninsu ba, sai nutsuwa ta sauka a
gare su, kuma rahama ta lulluɓesu, Mala'iku sun kewaye su, kuma
Allah Ya ambace su a cikin waɗanda ke wurin sa".
Muslim ne ya ruwaitoshi (2699).
Ladan Sanar Da Ilimi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Idan mutum ya mutu akin sa ya yanke sai dai daga abu uku:
Sadaka mai gudana, ko wani ilimi da ake anfanuwa da shi, ko ɗa na
gari da ya ke masa addu'a".
Muslim ne ya ruwaitoshi (1631).
4
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - lallai cewa Manzon Allah -
tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi - ya ce:
"Wanda ya yi kira zuwa ga shiriya yana da lada kwatankwacin
ladan wanda ya bi shi, ba za'a rage komai daga ladan su ba, kuma
wanda ya yi kira zuwa ga ɓata a kan sa akwai kwatankwacin zunubin
wanda ya bi shi, ba za'a rage komai daga zunuban su ba.
Muslim ne ya ruwaito shi (2674).
Daga Abu Mas'ud Al-Ansary - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon
Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Duk wanda ya shiryar akan wani aikin alheri, to, yana da
kwatankwacin ladan wanda ya aikata shi".
Muslim ne ya ruwaito shi (1893).
Ladan Alwala Da Cikata
Daga Abu huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Idan bawa musulmi ya yi alwala, ko kuma mumini, sai ya wanke
fuskar sa, to, kowane kuskure da ya kalla da idanun sa zai fice daga
fuskar sa tare da ruwa, ko kuma tare da ƙarshen ɗigon ruwa, idan ya
wanke hannayen sa, kowane kuskure zai fita daga hannayen sa
waɗanda hannayen sa suka damƙa da su tare da ruwa ko tare da
ƙarshen ɗigon ruwa, idan ya wanke kafafuwan sa kowane kuskuren
da kafafuwan sa suka tafi gareta zasu fita tare da ruwa ko tare da
ƙarshen ɗigon ruwa har sai ya fita tsarkakakke daga zunubai".
Muslim ne ya ruwaito shi (244).
التعليقات
لا توجد تعليقات بعد. كن أول من يشارك بتأمّل نافع.
ذات صلة
عظماء في التاريخ
islamicmedia.tv
1 view · 9 hours ago
من أحكام صلاة المرأة في الحرمين
islamicmedia.tv
1 view · 9 hours ago
البرنامج اليومي للمسلمة في شهر رمضان
islamicmedia.tv
1 view · 9 hours ago
أحكام المرأة في الصلاة دراسة فقهية مقارنة
islamicmedia.tv
1 view · 9 hours ago
توحيد الألوهية أساس الإسلام
islamicmedia.tv
1 view · 9 hours ago
شرح رسالة القواعد الأربع
islamicmedia.tv
1 view · 9 hours ago
توحيد الرب
islamicmedia.tv
1 view · 9 hours ago
شرح خطبة الحاجة
islamicmedia.tv
1 view · 9 hours ago
إِلاَّ لِيَعْبُدُونِ - كيف يوحد القرآن وجهة الإنسان؟
islamicmedia.tv
1 view · 9 hours ago
Resumo do livro Seleção de Hadiths Proféticos
islamicmedia.tv
1 view · 1 day ago