LibraryDokumen
Tauhidi Haqqin Allah A Kan Bayinsa
Littafine mai magana akan tauhidi da rabaraban tauhidi da kuma cewa Tauhidi Haqqin Allahne A Kan Bayinsa da sauransu By: Umar Muhammad Labdo Source: IslamHouse.com · Umar Muhammad Labdo
Dari buku
Halaman-halaman awal teks. Buka buku di atas untuk membacanya secara lengkap.
1
Jerin Littafan Shi’a Na 12
Tauhidi
Haqqin Allah A Kan Bayinsa
Umar Labxo
Manzu (SAW) ya ce
“Ya Mu’azu, shin ko ka san haqqin Allah a kan bayinsa? Mu’azu ya ce: Allah da Manzonsa
ne mafi sani. Manzo (SAW) ya ce: Haqqinsa shi ne su bauta masa shi kaxai, kada su haxa shi
da kome a wajen bauta. Sa’an nan ya ce: Shin ko ka san haqqinsu a kan Ubangiji? Mu’azu ya
ce: Allah da Manzo ne mafi sani. Ya ce: Kada ya yi musu azaba idan sun kaxaita shi da
bauta.”
(Bukhari da Muslim)
3
بسم هللا الرحمن الرحيم
Gabatarwa
Lallai godiya ta tabbata ga Allah, muna gode masa, muna neman taimakonsa, muna neman gafara tasa. Muna
neman tsari da Allah daga sharrin kawunanmu da miyagun ayyukanmu. Wanda Allah ya shirye shi, babu mai vatar
da shi kuma wanda ya vatar babu mai shiriya tasa. Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kaxai,
ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa Muhammad bawansa ne, kuma Ma’aikinsa ne. Tsira da aminci su
tabbata a gare shi, da Alayensa, da Sahabbansa, da waxanda suka bi Sunnarsa har zuwa ranar sakamako.
Bayan haka, babu shakka sanin ilmin Tauhidi shi ne wajibi na farko, kuma mafi muhimmanci a kan bawa
mukallafi, kamar yadda Allah Maxaukaki ya ce, “Saboda haka ka sani cewa babu abin bautawa face Allah.” (Suratu
Mahammad: 19). Sanin cewa babu abin bautawa sai Allah, wanda shi ne sanin Tauhidi, yana gaba da sanin sallah da
zakka da azumi da hajji da dukkan ibadojin Musulunci da shari’o’insa, da dokokinsa da tsare-tsarensa. Domin
Tauhidi shi ne ruhin Musulunci kuma shi ne harsashe wanda ake aza ginin addini a kansa. Ibada, kome kyawunta da
yawanta da ingancinta, idan ba’a xora ta a kan ingantaccen harsashe na Tauhidi ba, to kamar jiki ne ba rai ko kuma
ginin da ba harsashe. Wannan ya sa malamai magabata suke buxe littafansu da bayanin Tauhidi, kamar yadda malam
mai Ahlari ya yi, inda yake cewa a farkon littafinsa, “Auwalu ma yajibu alal mukallafi tas’hihu imanihi,” ma’ana:
“Farkon abinda yake wajaba a kan mukallafi shi ne inganta imaninsa.” Hanya guda ta inganta imani kuwa ita ce sanin
ilmin Tauhidi.
Wannan littafi da nake gabatarwa a yau, wanda kuma na sanya shi ya zama cikamakin Jerin Littafan Shi’a, an
buga shi da farko a shekarar 2005 a matsayin littafi mai zaman kansa. Amma na ga ya dace in sanya shi a cikin
wannan Jerin saboda ya zama qarin bayani ga aqidar Ahalus Sunna wal Jama’a kuma ya zama ciko ga maudu’in
littafin da ya gabace shi a Jerin. Hakan kuma, har yau, zai dace da qa’idar tarbiyya da take cewa idan ka koya wa
mutane cewa kaza ba shi da kyau, to sai ka ba su madadinsa mai kyau, wanda zai maye masa, ya cike gurbinsa.
Tauhidi a bisa tafarkin Sunna da magabatan al’umma na qwarai shi ne madadi mafi alheri ga aqidar Shi’a.
Komentar
Belum ada komentar. Jadilah yang pertama berbagi renungan yang bermanfaat.
Terkait
Tauhidi Daga cikin hudubobin masallacin Annabi
islamicmedia.tv
6 views · 5 months ago
TAMBAYA 100 DA AMSARSU (A CIKIN AKIDAR TAUHIDI)
islamicmedia.tv
8 views · 5 months ago
TAUHIDI WALLAFAR
islamicmedia.tv
7 views · 5 months ago
KUNDIN IMANI WANDA ALLAH YA WAJABTASHI AKAN BAYINSA NA ABINDA YA ZO A ALKUR'ANI MAI GIRMA DA SUNNAR
islamicmedia.tv
5 views · 5 months ago
KATARI WAJEN FAHIMTAR TAUHIDI
islamicmedia.tv
7 views · 5 months ago
Kare Tauhidi
islamicmedia.tv
7 views · 5 months ago
MFULULIZO WA MAKALA JUU YA KULINDA TAUHIDI
islamicmedia.tv
8 views · 5 months ago
Wajabcin Yaqar Bidi’a
islamicmedia.tv
6 views · 5 months ago
Mugun Nufin ‘Yan Shi’a ga Al’umma
islamicmedia.tv
5 views · 5 months ago
Matsayin Musulmi a wajen ‘Yan Shi’a
islamicmedia.tv
8 views · 5 months ago