SHARHIN LITTAFIN (MUHIMMAN DARUSSA GA DAUKACIN AL'UMMAH)
admin·5 views·5 months ago SHARHIN LITTAFIN (MUHIMMAN DARUSSA GA DAUKACIN AL'UMMAH): Littafi ne da harshen HAUSA wanda Dr. Haisam Sarhaan ya tanade shi, domin sharha ga littafin AD-DURUSUL MUHIMMA LI AMATIL UMMAH, na Imam Ibnu-Baaz -Allah ya yi rahama a gare shi-, Mawallafin (Shaikh Haisam) ya tattara nau'ukan ilmomin shari'a a cikin littafin, musamman wadanda suka ta'allaka da hukunce-hukuncen fikihu, da akida, da halayya, wadanda ya dace ga daukacin al'ummah su sansu. Kuma Mawallafin ya sanya littafin cikin wani tsari mai kyau, ta fiskar sanya shi cikin jadwala, da rarraba shi daki-daki, Kuma ya ambaci muhimman manufofin addini, da dunkulallun ma'anoni, Kuma a bayan kammala kowane yanki na littafin, Mawallafin ya tsara tambayoyi da jarrabawan da suka ta'allaka da wannan babin, Kuma ya ambaci dukkan wadannan ne; ba tare da takaicewar da zata cire wasu fa'idodi ba, ko tsawaitawa mai gajiyarwa mai sanya kosawa.
Source: IslamHouse.com
Extrait du livre
Les premières pages du texte. Ouvrez le livre ci-dessus pour le lire en entier.
()الدروس المهمة لعامة الأمة
“Muhimman darussa ga daukacin Al-umma”
Dr. Haisam dan Muhammadu Jamil Sarhan
Dr. Abubakar Hamza Zakariyya Misau
2020 = 1442AH
Bayan haka: Wadannan takaitattun kalmomi ne, dangane da
abinda ya wajaba ga dukan Mutane su sani game da addinin
Musulumci. Na sanya masa suna (MUHIMMAN DARUSSA GA
DUKAN AL'UMMA).
Shehin Malami Abdul'aziz dan Abdullahi bn Baaz – - ya ce:
Da sunan Allah Mai rahama Mai jin-kai! Godiya ta
tabbata ga Allah Ubangijin Talikai. Kyakkyawar makoma ta masu
tsoron Allah ce. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga
BawanSa kuma ManzonSa Annabinmu Muhammadu, da Iyalan
gidanSa da SahabbanSa baki daya.
Ina rokon Allah ya amfanar da Musulmai da su, kuma Ya
karba min; lallai Shi Mai kyauta ne Mai karamci.
Saboda darussan suna da muhimmanci, kamar yadda
Mawallafin littafin – - ya basu suna, kuma Maluma sun yi nasiha
kan karanta su.
Da mai Magana zai ce: E, darussan suna da muhimmanci,
amma ga Mutane gama-gari, ba daliban ilimi ba, saboda jin cewa
martabarsa ta ketare ta gama-garin Mutane!
Amsa: Za mu masa tambaya kan abinda littafin kunsa, idan har
bai sansu ba, to gama-garin Mutane sun fi shi alheri. Kuma Dalibin
ilimi ya dace ya zama mai tawali'u, kuma kada ya yi girman kai ga ilimi
da Maluma, sai kuma ya tafi akan tafarkin da Malaman Allah suka tafi
a kai. Ya zo cikin Sahihul Bukhariy: Mujahid ya ce: MAI KUNYA DA
MAI GIRMAN KAI BA SU KOYAN ILIMI.
‘
‘