LibraryDocuments
Auren Mutu’a a wajen Yan Shi’a
littafi mai mahimmanci akan Auren Mutu’a a wajen Yan Shi’a da matsayin musulunci dangane da wannan auran da sauransu By: Umar Muhammad Labdo Source: IslamHouse.com · Umar Muhammad Labdo
Extrait du livre
Les premières pages du texte. Ouvrez le livre ci-dessus pour le lire en entier.
1
Jerin Littafan Shi’a Na 4
Auren Mutu’a
a wajen
‘Yan Shi’a
Umar Labxo
2
بسم هللا الرحمن الرحيم
Ma’anar Mutu’a: Auren Wucin Gadi
Mutu’a, ko kuma auren wucin gadi, watau auren da ba na dun-dun-
dun ba, ma’anarsa shi ne namiji ya qulla jinga da mace cewa zai sadu da ita
sau xaya ko sau biyu, ko kuma na tsawon awa xaya, ko kwana kaza, ko wata
kaza, a kan kuxi kaza ko ladan abu kaza.
Auren Mutu’a yana cikin aurace-auracen Jahiliya kuma an yi aiki da
shi a farkon Musulunci kana daga bisani aka haramta shi. An karvo ruwaya
daga Ali binu Abi Xalib (R.A), cewa “Manzon Allah (SAW) ya hana auren
Mutu’a da cin naman jakin gida a lokacin (yaqin) Khaibar.”1
Amma ‘yan Shi’a sun ci gaba da halasta Mutu’a kuma sun qago
ruwayoyin qarya waxanda suka nuna falalarta da xumbin ladan wanda ya yi
ta, da kuma darajarsa a aljanna. Babu shakka sun yi haka domin su vata
al’ummar Musulmi ta hanyar yaxa lalata da varna da alfasha a tsakaninsu
kuma don su jawo hankalin jahilai, musamman matasa, zuwa ga tafarkinsu.
Falalar Mutu’a
Akwai xaruruwan ruwayoyi a cikin littafan malaman Shi’a da suke
izna da su waxanda suke nuna falalar auren wucin gadi. Ya zo a cikin
littafin Man La Yahduruhul Faqih, xaya daga cikin littafansu guda huxu
mafiya inganci, sun laqa ma Ja’afar Sadiq, Imaminsu na shida, cewa ya ce:
“Lallai Mutu’a addinina ce kuma addinin iyayena. Wanda ya yi aiki da ita
1 Bukhari da Muslim.
3
ya yi aiki da addininmu kuma wanda ya yi inkarin ta ya yi inkarin
addininmu, kuma ya yi riqo da wanin addininmu.”1
Ya zo a wannan littafi har yau, sun dangana ga Annabi (SAW) cewa
wai ya ce: “Wanda ya yi Mutu’a sau xaya zai amince fushin Allah, wanda
ya yi Mutu’a sau biyu za’a tashe shi tare da zavavvun bayi, wanda ya yi
Mutu’a sau uku zai haxa kafaxa da ni a aljanna.”2 A wata ruwayar mai kama
da wannan, sun qaga wa Manzon Allah (SAW) cewa wai ya ce: “Wanda ya
yi Mutu’a sau xaya za ta zama (gare shi) kamar darajar Hussaini (A.S);
wanda ya yi Mutu’a sau biyu darajarsa kamar darajar Hassan (A.S) ce;
wanda ya yi Mutu’a sau uku darajarsa za ta kasance kamar darajar Ali (A.S);
kuma wanda ya yi Mutu’a sau huxu darajarsa kamar darajata ce.”3
Da yake mata suna da qarin kunya a kan maza, wataqila za su buqaci
a qara xan ingiza su kaxan kafin su faxa ramin alfasha. Don haka
Alqummi, wanda suke yi wa laqabi da Alsaduq (watau mai yawan gaskiya!)
ya kitsa musu tasu ruwaya ta musamman. Ya ce, “Lokacin da aka yi isra’i
da Annabi (SAW) zuwa sama, ya ce: Jibrilu ya riske ni ya ce: Ya
Muhammad, Allah mai girma da xaukaka yana cewa: Lallai ni na gafartawa
masu yin Mutu’a daga matayen al’ummarka.”4
Ladan Mai Yin Mutu’a
Abinda ya gabata dangane da falala da xaukakar darajar mai yin auren
Mutu’a ne. Amma dangane da xumbin ladan da zai samu, bari mu saurari
Alsaduq ya qara shara mana ita. Ya ce: an tambayi Abu Abdullahi, watau
1 Ibnu Babawaih Alkummi, Man La Yahduruhul Fakih, bugun Darut Ta’aruf, Bairut, 1401 B.H.,
mujalladi na 3 shafi na 336.
2 A duba Man La Yahduruhul Fakih na Alkummi, muj. na 3 sha. 336.
3 Fatahallah Kashani, Tafsiru Minhajis Sadikin, bugun Maktabatus Sadar, Tehran-Iran, 1379 B.H., muj.
na 2 sha. na 493.
4 A duba Man La Yahduruhul Fakih, muj. na 3 sha. na 463.
Commentaires
Aucun commentaire pour l'instant. Soyez le premier à partager une réflexion utile.
À voir aussi
Wajabcin Yaqar Bidi’a
islamicmedia.tv
6 views · 5 months ago
Mugun Nufin ‘Yan Shi’a ga Al’umma
islamicmedia.tv
5 views · 5 months ago
Matsayin Musulmi a wajen ‘Yan Shi’a
islamicmedia.tv
8 views · 5 months ago
Aqidar Ahalus Sunna
islamicmedia.tv
4 views · 5 months ago
Aqidar Khumaini da Koyarwarsa
islamicmedia.tv
4 views · 5 months ago
Zuwan Shi’a Nijeria
islamicmedia.tv
6 views · 5 months ago
Ahalul Baiti a mahangar Yan Shi’a da Ahalus Sunna
islamicmedia.tv
6 views · 5 months ago
Tauhidi Haqqin Allah A Kan Bayinsa
islamicmedia.tv
6 views · 5 months ago
WA YA KASHE HUSSAINI?
islamicmedia.tv
7 views · 5 months ago
Aqidar ‘Yan Shi’a dangane da Sahabbai
islamicmedia.tv
6 views · 5 months ago