Libraryوثائق
KUNDIN IMANI WANDA ALLAH YA WAJABTASHI AKAN BAYINSA NA ABINDA YA ZO A ALKUR'ANI MAI GIRMA DA SUNNAR
KUNDIN IMANI WANDA ALLAH YA WAJABTASHI AKAN BAYINSA NA ABINDA YA ZO A ALKUR'ANI MAI GIRMA DA SUNNAR ANNABI Source: IslamHouse.com
من الكتاب
الصفحات الأولى من النص. افتح الكتاب أعلاه لقراءته كاملًا.
KUNDIN IMANI WANDA
ALLAH YA WAJABTASHI
AKAN BAYINSA NA ABINDA
YA ZO A ALKUR'ANI MAI
GIRMA DA SUNNAR ANNABI
4
A gabanin littafin
Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin ƙai
Godiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya saukar da littafi ga
bawanSa, bai sanya karkata a gare shi ba, ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai Yake ba Shi da abokin
tarayya, mulki naSa ne, kuma godiya ta tabbata gareShi, Shi Mai iko
ne akan dukkan komai, ina shaidawa cewa (Annabi) Muhammadu
bawanSa ne kuma ManzonSa ne kuma amintaccenSa ne akan
wahayinSa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -.
Bayan haka: Lallai ilimin Akida shi ne mafi daukakar ilimai kuma
mafi girmansu; domin shi yana magana ne ga mafi daukakar abin
sani - shi ne Allah tsarki ya tabbatar maSa -, kuma mafi daukakar
abin nufi - shi ne kadaitaShi da yin imani da Shi - kuma mafi
daukakar makoma - shi ne ganin Ubangiji Mai girma a gidan ni'ima,
da bin Annabi mai girma - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi
-, da bin hanya madaidaiciya; saboda haka mukayi kwadayin wallafa
wani littafi wanda ya tattaro mas'alolin Akida wanda muke neman
shiriya da shi a cikinsa da littafin Allah, da sunnar AnnabinSa - tsira
da amincin Allah su tabbata agare shi, wanda ya yi nesa daga
zantukan ma'abota zance fararru, da Ta'arifai da Rukunai da
Sharudda, kuma zamu sanya shi a hannun kowa ta inda malami da
dalibain ilimi a jami'o'i da waninsu zasu amfana daga gare shi , kai
dama dukkan musulmai.
Dalilin wallafa littafin:
Hakika magabatamu na gari sun yi babban kokari a bayanin
ingantacciyar Akidah, da kuma bayanin abinda yake kishiyantarta,
da yin raddi ga wadanda suka saba. Hakika wannan littafin ya zo
dan ya kusanto da abinda magabata suka wallafa ga daliban ilimi
dama dukkanin musulmai; ta inda muka hado mas'alolin Akidah a
cikin littafi daya wanda ya tattarosu, mun takaita tabbatar da
ingantacciyar Akida banda kutsawa a cikin raddi, kamar yadda muka
yi kwadayi akan yinsa da saukakan haruffa bayyanannu, da kuma
jeranta shi irin na tsari mai ban kaye, muna fatan mu kasance da
hakan mun tabbatar da manufofi biyu: Na dayansu: Bada
5
gudunmawa a cikin kusanto da ilimummukan magabata. Na karshen
kuma: toshe bukata mai tsanani a dakin karatun Akidah, ita ce:
Samar da sassaukan littafi mai sassaukan lafuzza, wanda ya tattaro
dukkan bincike-binciken Akidah.
Tsarin da muka bi a wallafawar:
Bijiro da ayoyi da hadisan da suke da alaka da kowanne bangare
daga bangarorin karatun Akidah, da tato shi daga garesu.
Bijiro da dukkanin bangarorin littattafan Akidu: Duk daya ne
masu isnadi ne ko kuma gundarin abubuwa ko sharhohin matanin;
dan tabbatar da cewa rairayowar da muka yi ga Akida daga ayoyi ne
da kuma hadisai, kuma mai kunshe ne ga abinda mawallafan
littattafan Akida suka wallafa.
Idan mas'ala ta akida ta zo a cikin AlKur'ani mai girma, ko a
sunnar Annabi ta fuska daya; zamu isu da dalili daya ko dalilai biyu
wanda ya zo a ambaton wannan mas'alar a cikinsu. Amma idan
mas'ala ta zo a cikin AlKur'ani mai girma ko sunnar Annabi ta fuskoki
da yawa - kamar siffar zance, da daukaka sama, da hannu, da ganin
muminai ga Ubangijinsu a farfajiyar Alkiyama da kuma aljanna - to
zamu lazimci ambaton dalili ta kowacce fuska daga fuskokin da suka
zo, amma ba zamu lazimci kawo dukkan abinda ke cikin babin ba.
Zamu iya bukatuwa da kawo sashin bangarorin mas'ala a wani babin,
sannan mu sake kawota mu kuma cikata a wani babin daban, kamar yadda
muka zo da labarin halittar Mala'iku a babin halitta, kuma muka cike zancen
game da su a cikin babin imani da Mala'iku, muka ambaci wasu ayoyi masu
nuni ta fuskoki (da dama) a cikin babin imani da samuwar Allah, kuma ita
kanta ayar zata iya zuwa ababin Rubibiyya dan kusancinsu, abin nufi daga
babin imani da samuwar Allah shi ne bayyanar da dalilan samuwar Ubangiji
wadanda mai musun samuwar Allah Yake inkarinsu, yayin da abin nufi daga
babin Rububiyya shi ne tabbatar da Rububiyya wacce ta lazimci Uluhiyyar
Allah wacce mushrikai suke jayayya a cikinta, kamar yadda zamu iya kawo
ayoyi masu girma ko hadisi madaukaki a cikin sama da guri daya,
gwargwadan fuskar kafa hujja da su, da kuma bukatuwa zuwa garesu.
Yayin bukatuwa zamu iya ambatan wasu abinda aka cirato daga
jagorori magabata wadanda suke bayyanar da abin nufi daga aya da
التعليقات
لا توجد تعليقات بعد. كن أول من يشارك بتأمّل نافع.
ذات صلة
Tauhidi Haqqin Allah A Kan Bayinsa
islamicmedia.tv
6 views · 5 months ago
abinda bai kamata musulmi ya jahilta acikin addinin sa ba
islamicmedia.tv
6 views · 5 months ago
ABINDA JAHILTARSA BAYA YIWUWA GA YARAN MUSULMAI (ABINDA YA KAMATA YARAN MUSULMAI SU SANSHI).
islamicmedia.tv
4 views · 5 months ago
Hukuncin Sihiri da Bokanci da abinda yake da alaƙa da su
islamicmedia.tv
4 views · 5 months ago
AƘIDA INGANTACCIYA DA ABINDA YAKE KISHIYANTAR TA
islamicmedia.tv
3 views · 5 months ago
عظماء في التاريخ
islamicmedia.tv
1 view · 10 hours ago
من أحكام صلاة المرأة في الحرمين
islamicmedia.tv
1 view · 10 hours ago
البرنامج اليومي للمسلمة في شهر رمضان
islamicmedia.tv
1 view · 10 hours ago
أحكام المرأة في الصلاة دراسة فقهية مقارنة
islamicmedia.tv
1 view · 10 hours ago
توحيد الألوهية أساس الإسلام
islamicmedia.tv
1 view · 10 hours ago